Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya amince da nadin sabuwar hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa.
Zubaida Umar ta zama sabuwar Darekta Janar ta wannan hukuma mai taimakawa wajen kai agajin kar-ta-kwana a Najeriya.
Ajuri Ngelale ya sanar da haka a matsayinsa na mai magana da yawun shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya dauko mutumin Buhari ya ba shi shugabancin hukumar kula da almajirai
Kamar yadda Ajuri Ngelale ya bayyana a jawabin da ya fitar a ranar Juma’a, nadin ya nuna za a dama da kowane jinsi a mulki.
Bola Tinubu ya nada Zubaida Umar ne a lokacin da ake kukan mata ba su samun mukamai da kujeru a gwamnati a Najeriya.
A tarihin hukumar NEMA da aka kafa tun 1999, ba a taba samun lokacin da mace ta jagorance ba sai a wannan karo.
Kamar yadda Olusegun Dada ya zayyano a dandalin X, sabuwar shugabar ta NEMA ta kware a bangarorin aiki da dama.
"Sabuwar Darekta Janar din ta shafe sama da shekaru 20 tana aiki a bangarori dabam-dabam,Ciki akwai kula da ma’aikata, harkokin kudi da gudanarwa. Tana cikin ‘yan cibiyar kwararrun ma’aikatan banki da cibiyar ba da lamuni.Tana da takardar shaidar ACCA a bangaren kula da dukiyar al’umma."Rashin tsaro: Rundunar soji ta saduda, ta nemi agajin EFCC a wasu bangarori, ta fadi dalili
- Ajuri Ngelale
Da wannan sabon nadi da aka yi, tsohuwar darektar bankin ba da lamunin gina gidaje za ta shiga ofis ba da wata-wata ba.
Yayin da ta canji Ahmed Habib, Bola Tinubu ya ce yana fatan Zubaida Umar za ta kawo sauyi kamar yadda aka gani a FMBN.
Rahoton nan ya tabbatar da mutane biyu suka samu mukami daga Kano a rana daya da Bola Tinubu ya tsige Hon. Sha’aban Sharada.
Nauyin kula da almajirai da marasa zuwa makarantun boko ya dawo hannun Janar Lawal Ja’afar Isa wanda ya yi gwamna a Kaduna.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbYB4hZVmnrCZnaOutbXNZquipqWXwm7AwGaqmqOVYq6rtdieZK2Zop61qnnMmpqeZaSWerStzK5krKClnK6jrc2coKdlnpq6onnBmrCapl2otaa3wKusZmplZA%3D%3D